Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Hukumar na son a dage zaben na tsawon wata daya, kuma ta ba da shawarar gudanar da zaben a ranar 24 ga watan Janairu bayan tuntubar majalisa.
Tunda farko dama an bayyana zaben mai cike da rashin tabbas idan akayi la’akari da yadda lokacinsa ke kara matsawo.
Har yanzu ba’a sanar da sunayen ‘yan takara na dindindin da zasu fafata a zaben, kana har yanzu akwai rarrabuwar kai tsakanin bangarorin dake rikici a kasar.
Lamarin da tuni masana ke ganin cewa zai iya kara jefa kasar cikin wani sabin rikici.
Libiya ta fada cikin ridani ne tun bayan guguwar neman sauyin da ta yi awan gaba da mulkin tsohon shugaban kasar mirigayi Muammar Ghaddafi a cikin shekarar 2011.
342/